Sunday, 11 August 2019

MARAWA ƳAN TA’ADDA BAYA: Matawalle ya tsige Sarkin Maru da Hakimin Kanoma

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tsige sarkin Maru, Abubakar Ibrahim daga kujerar sarautar Maru.


Tare da sarkin Maru, gwamna Matawalle ya tsige hakimin Kanoma, Ahmed Lawal a dalilin hannu da aka kama su dashi dumu-dumu wajen marawa ƴan ta’adda da ta’addanci baya a jihar.

Idan ba a manta ba a cikin watan Yuli ne gwamna Matawalle ya bada sanarwar dakatar da sarkin Maru Abubakar Ibrahim daga kujerar sarautar Maru.

Sanarwar ya ce gwamna yayi hakane bayan gano cewa sarkin na da hannu dumu-dumu a ayyukan mahara da yayi wa jihar katutu.

Bayan haka duk a wannan lokaci an dakatar da hakimin Kanoma, Ahmed Lawan shima bisa ga irin wannan zargi shima.

Tun bayan rantsar da Matawalle jihar Zamfara ta ɗau saiti ya maida hankalin sa kacokan wajen dawo da martabar jihar kamar yadda aka santa a da.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment