Sunday, 4 August 2019

Mun kama Sowore kan yunkurin kifar da gwamnati>>SSS

Jami'an hukumar tsaron ta farin kaya wato SSS, yayin wani taron manema labarai da suka yi a Abuja, ranar Lahadi, sun ce sun kama Omoyele Sowore, mai kamfanin jaridar Sahara Reporters ta intanet kan shelar da ya yi ta #RevolutionNow da ke nufin juyin juya-hali.


Mai magana da yawun hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya, ya ce suna da cikakkiyar masaniya kan 'goyon bayan' da Mista Sowore yake samu daga kasashen waje da nufin tayar da tarzoma a Najeriya ta hanyar shelar da ya yi ta 'samar da sauyi a kasar'.

Sai dai jami'in hukumar bai fadi ko yaushe ne za a gurfanar da mista Sowore a gaban kotu ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment