Saturday, 10 August 2019

Mutane sun shiga halin matsi bayan da aka dauke wuta a Birtaniya

Kamfanin da ke rarraba wutar ya ce akwai darussan da zai dauka sakamakon daukewar wutar da ya janyo mutum kusan miliyan daya suka shiga cikin duhu, a Ingila da Wales ranar Juma'a.


Darekata mai kula da ayyuka na kamfanin, Duncan Burt ya shaida wa BBC cewa injinan samar da wutar sun yi aiki yadda ya kamata, bayan da tashoshin bayar da wutar guda biyu suka samu tangarda.

Ya ce bai yadda cewa hari aka kai musu ta intanet ba, ko kuma a dora alhakin hakan ga rashin tabbas dangane da injinan samar da wuta daga iska ba.

Tuni dai kamfanin ya umarci a yi bincike dangane da hakikanin abin da ya faru.Kamfanin ya ce zai dauki mataki dangane da abubuwan da suka biyo bayan daukewar wutar da suka hada da yadda fasinjoji suka rasa jirgin kasa da rincabewar yanayin ababan hawa sakamakon daukewar wutar da ke bayar da hannu da kuma yadda dubban mutane suka rasa wuta a gidajensu.

Har zuwa safiyar Asabar din nan dai wasu hanyoyin babu jiragen na kasa saboda rashin wutar.

Daukewar wutar dai ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma'a, inda kusan ilahirin yankunan Ingila da Wales suka kasance cikin duhu.

To sai dai wutar ta dawo a wasu sassan bayan minti 40 da kasancewa cikin duhu dundim.

Daya daga cikin manyan tashoshin jirgin kasa da ke birnin London, King's Cross na daya daga cikin wuraren da rashin wutar ya shafa matuka, inda aka kwashe awanni ba tare da jirgi ya tashi ko ya shiga tashar ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment