Wednesday, 14 August 2019

Mutum biyu sun warke daga cutar Ebola


oth survivors are the wife and child one of the three Ebola deaths in Goma last month
An sallami mutum biyu da aka yi wa maganin cutar Ebola daga wata cibiyar gwaji a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, bayan sun warke daga cutar.


Mutanen suna cikin mutanen da ke fama da cutar a garin Goma, wato garin da ya fi fama da annobar inda mutum 1,800 suka mutu.
Sai dai akwai wasu mutum biyu da aka yi gwajin a kansu kuma suka rasa ransu sanadiyyar cutar.
Masana kimiyya sun ce suna da kwarin gwiwar cewa ana gab da samun rigakafin cutar bayan samun nasarar da aka yi wajen gwajin maganin cutar nau'ika biyu, in ji Dokta Sabue Mulangu.
Har ila yau ya ce yana ganin zuwa gaba kaso 60 cikin mutum 681 da suka kamu da cutar za su tsira.
Masu binciken sun ce idan aka fara yin magani da wuri, kaso 90 cikin 100 ne na wadanda suka kamu da cutar za su tsira, idan suka yi amfani da magungunan REGN-EB3 da kuma mAb114.
An samar da magungunan ne daga kwayoyin yaki da cutar da aka samu a jikin wadanda suka tsira daga ita.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ce ta jagoranci gwajin magungunan kuma yanzu masu binciken sun yarda a fara amfani da magungunan ga duk wani da ke fama da cutar.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment