Saturday, 10 August 2019

Na fi jin dadin aikin hajji cikin talakawa>>Gwamnan Bauchi


Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya ce shi da wasu mukarrabansa da suke aikin hajjin bana suna zaune ne a gidan alhazai gama-gari na jihar, maimakon masauki ko otal na kasaita domin hakan ya fi dadi da lada, kuma ta hakan zai san matsalolin alhazan don magance su.


A wata hira da ya yi da BBC ta waya ya ce, daga kasa mai tsarkin, gwamnan ya ce zama cikin alhazai talakawa shi ne mafi alheri a wurinsa maimakon warewa a wani masauki na kasaita.
Gwamnan ya ce a baya yakan je aikin hajjin ne ya kasance cikin tawaga ta manya da kan sauka a manya-manyan otal na kasaita irin su Hilton, ba ya shiga cikin alhazai gama-gari da kan zauna a masauki irin su Masfala, a yi tafiya ta kusan kilomita 4 zuwa 5 a kasa, kafa na ciwo, kuma ana ganin yadda kowa yake fama.
Amma yanzu sai ya yanke shawara ya shiga cikin sauran alhazai da kan cakudu da juna, tun bayan da a wata shekara a baya ya yi irin wannan cakuduwa har ma ya zama jagoran tawagarsu a motar da suka shiga.
Ya ce wannan ne ya sa ya ce yanzu ya kamata ya dada komawa aikin hajjin, ya kasance tare da mutanen da suka zabe shi ko a dalilin hakan za a gane abubawan da suke sa alhazai su kasance cikin mawuyacin hali na rashin kulawa da sauransu, wanda ya ce kuma ta hakan ya fahimci wannan ne sila saboda rashin sa ido a kan lamarin.
Sanata Balan ya ce idan ya kwatanta zuwansa hajjin irin na manya da kuma na alhazai gama-gari, ya gane cewa a shiga ta manya ba ka haduwa da mutane sosai,
wanda hakan ma sai ya ce yana gani kamar ma ba aikin hajjin mutum ya yi ba yanda zai ji dadi, ya sadu da sauran jama'a na wasu jihohin Najeriya da ma na wasu kasashen duniya, a yi zumunta da mu'amulla da juna, a dauki hoto tare da sauransu.
Amma kuma a yanzu da ya yi hakan ya hadu da mutanen da ya dade bai sadu da su ba, amma idan mutum ya je a tawagar manya ana ta binsa da jami'an tsaro, duk ba zai samu damar yin hakan ba.
Game da wani hoto da ya sanya a Instagram, wanda a ka gan shi yana yi wa wani aski, a can, ya ce, daman ya saba da haka, yakan je da almakashinsa ya rika yi wa mutane saisaye su ma su yi masa, saboda hakan ma yana da lada, kamar yadda ya koyi hakan kuma yake yi tun suna makarantar sakanadare.
Gwamnan ya ce sun bullo da wani shiri domin kyautata wa alhazansu, inda suka kai mata goma da domin yi wa alhazan jihar masa 'yar Bauchi a yayin zaman Mina, da kuma nufin sama wa mutanensu aikin yi, kuma fatansu shi ne a dalilin hakan ma wasu jihohin Najeriyar su san masar 'yar Bauchi.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment