Saturday, 24 August 2019

Najeriya za ta karbi biyan bashin Naira biliyan 614 daga jihohinta 35

Gwamnatin Najeriya ta fara wani shirin tattaro kudaden lamunin da ta arawa jihohin kasar 35 ban da jihar Lagos wadanda yawansu ya kai Naira biliyan 614, matakin da ke zuwa kammala rantsar da ministocin kasar karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari.

Acewar ministar kudi kasafi da tsare-tsare a Najeriya Zainab Ahmad tuni taron kolin tattalin arziki a ranar alhamis karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya amince da kafa wata tawaga daga kungiyar gwamnonin kasar wadanda za su gana da babban bankin kasar don fara daukar matakin dawo da kuydaden.

Rahotanni sun bayyana cewa kowacce jiha cikin jihohin 35 ta karfi kudin da yawansa ya kai Naira biliyan 17 da rabi in banda jihar Lagos.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment