Sunday, 11 August 2019

Premier League: Man City ta lallasa West Ham 5-0

A wasan da Manchester City da West Ham suka buga a jiya, City ta lallasa West Ham da ci 5-0 inda Raheem Sterling ya ci kwallaye 3 shi kadai.A karin farko an fara amfani da na'urar nan dake taimakawa Rafali da ake kira da VAR a gasar Premier inda wata Kwallo da Gabriel Jesus yaci bayan ta farko da yaci aka kashe ta saboda Sterling yayi satar gida.

Sannan An sa Aguero ya sake bugun daga kai sai me tsaron gida bayan da golan West Ham ya fita daga kan layi a bugun farko da Agueron ya barar, amma a bugu na biyu sai Agueron ya ci kwallon tashi.

Hakanan a jiyanne dai aka buga wasa tsakanin Tottenham da Aston Villa inda kwallon wuri da Macginn ya ciwa Aston Villa ana mintuna 9 da take wasa ta so ta makalewa Tottenham.

Saidai ana mintuna 73 da wasane Ndombele ya ramawa Tottenham kwallonta sannan daf da za'a tashi Kane ya ci kwallaye 2, haka aka tashi wasan 3-1.

Ga sakamakon wasannin da aka buga jiya, Kamar Haka:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment