Friday, 9 August 2019

Premier League:Liverpool ta ci Norwich 4-1

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta fara gasar cin kofin Premier League ta bana da kafar dama bayan data lallasa Norwich da ci 4-1 a wasan farko na gasar ta kakar 2019/20 da suka buga da yammacin yau.



Mohamed Salah, Origi, Van Dijk da Hanley ne suka ciwa Liverpool kwallayenta.

A wasan na yau, Salah ya kafa sabon tarihi inda a kungiyoyi 23 daya fuskanta a gasar Premier League tun zuwanshi Liverpool daga AS Roma ya ci kungiyoyi 21 kenan zuwan yanzu, inda Kungiyoyin Manchester United da Swansea ne kawai suka rage be taba ci ba.

Sannan Salah ya zamo na biyu da yafi bayar da taimako aka ci kwallo a gaba dayan manyan gasannin kwallo da ake bugawa a turai inda ya bayar da taimako aka ci kwallo sau 12 kenan daga kakar 2017/18, Neymar ne kadai ke gabanshi da bayar da taimako sau 13.

Salah dinne dai ya kawo kwallon da Van Dijk ya ci da kai ta yau




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment