Tuesday, 6 August 2019

PSG ta wa Man United tayin Neymar amma sunce basa so: Madrid kuma ta dukufa a batashi


Kungiyar kwallon kafa ta PSG na son sayar da dan wasanta, Neymar kamar yanda shima dan wasan ke son barin kungiyar amma alamu sun nuna ba zasu samu nasarar sayar dashi akan Yuro 180 ba saidai watakila su bayar dashi aro.Neymar dai nason komawa tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona ne Saidai kudinshi na daya daga cikin aninda zasu bashi matsala, hakan yasa PSG ta fara neman kungiyar da zata badashi aro kuma tawa Manchester United tayi amma Man United din tace bata so.

PSG ta lura cewa rashin jituwar dake tsakanin Neymar da masu gudanarwar kungiyar abin bana sasantawa bane shiyasa take son samun mafita akanshi kamin fara kakar wasan League 1 a karshen makonnan da muke ciki.

Wani rahoton kuma na cewa Real Madrid ma ta dawo neman Neymar din saidai a wannan karin tana so PSG ta bata shi a matsayin aro, Kamar yanda Diario Gol ta ruwaito.

Saidai Sport ta ruwaito cewa, shugaban Real Madrid, Florentino Perez ne ke son kawo Neymar a yayin da shi kuma kocin Madrid din, Zinedine Zidane Pogba yake son su siya.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment