Saturday, 24 August 2019

PSG zata biya tara saboda zagin Neymar da magoya bayanta suka yi

Hukumar shiryawa da kuma lura da gasar Ligue 1 ta Faransa LFP, ta ci tarar kungiyar PSG euro 2,000, saboda yadda magoya bayanta suka rika zagi da furta sauran kalamai na batanci kan Neymar, yayin wasan da suka doke Nimes.

Nuna zazzafar adawar da magoya bayan PSG suka yi ga Neymar ya auku ne a ranar 11 gawatan Agustan da muke ciki, lokacin da suka samu nasarar doke Nimes da kwallaye 3-0.

An samu tsamin dagantaka tsakanin Neymar da magoya bayan PSG ne tun bayan da dan wasan ya fito karara ya bayyana aniyar komawatsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, lamarin da ya kai ga Neymar din ya kauracewa yin atasaye tare da tawagar kungiyar tasata PSG yayin wasannin sharara fagen soma kakar wasa ta bana.

Har yanzu dai dan wasan bai buga PSG wasa a kaka ta bana ba, lamarin dake da alaka, da shirin komawarsa Barcelona Ko Real Madrid a kowane lokaci daga yanzu, kafin rufe hada-adarsauyin shekar ‘yan wasa a ranar 2 gawatan Satumba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment