Saturday, 24 August 2019

Real Madrid ta yi kunnen doki da Real Villadolid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a wasan data buga na farko a gidanta a kakar bana ta gasar Laliga tsakaninta da Real Villadolid sun tashi kunnen doki 1-1.
Karim Benzema yayi kokari inda ya ciwa Madrid kwallo ana mintuna 82 da wasa,saidai Villadolid ta farke kwallon ta hannun dan wasanta, Guardiola wanda yaci kwallon ta hanyar sakawa golan Madrid, Thibaut Courtois kwallon a Osi.

Courtois yayi kokari sosai a wasan na yau dan kuwa ya tare kwallayen da da ace yayi sakaci da an cisu kuma masoya kungiyar da yawa sun Yaba mai, saidai kwallon karshe da Guardiola ya cishi ta Osi ta dauki hankula sosai inda wasu suka hau shafukan sada zumunta suna mai ba'a, ganin cewa dama an saba cinshi irin wannan kwallon a baya.

Wani abin lura a wannan wasa shine a karo na biyu a jere,Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane yayi amfani da Gareth Bale wanda hakan ke nuna cewa tsamar dake tsakaninsu ta kau.

Kalli cin da akawai Courtois a kasa:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment