Monday, 12 August 2019

SAMA DA FURSUNONI DUBU BIYU GWAMNA GANDUJE YA SAMARWA ƳANCI A JIHAR KANO

Domin samar da ƴanci da walwalar gudanar da shagulgulan bukukuwan babbar Sallah, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya kai wata ziyara ta musamman gidajen yari (Prisons) guda goma na Jihar Kano inda ya sa aka fitar da ɗaurarru kimanin mutum (200) biyo bayan samar musu ƴanci da ya yi domin su ma su samu sukuni da damar yin bukukuwan Sallah cikin iyalansu.


Da ya ke tsokaci game da dalilan sakin nasu, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa "an ƴanta wasu daga cikinsu ne a dalilin tsufansu. Wasu kuma a dalilin rashin lafiyar da su ke fama da ita. Wasu kuwa saboda gwamnati ta jibinci lamarin biya musu haƙƙoƙin da ke kansu".

Inda kuma mai girma gwamna ya ƙara da yi musu gargaɗi da jan hankali da su kasance masu gyara kura-kuransu na baya su zama mutane nagari waɗanda al'umma za ta yi alfahari da su.

Kuma nan take bayan sakin nasu, gwamna Ganduje ya ba su gudunmawar kuɗi naira dubu biyar-biyar domin su samu dama da sukunin isa muhallansu.

Daga lokacin fara wannan shiri na afuwa zuwa yau, kimanin fursunoni (2,717) ne gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ƴanta a lokutan bukukuwan Sallah daban-daban.

A nasa tsokacin, shugaban hukumar gidajen yari ta Jihar Kano, Mista Magaji Ahmad Abdullahi, ya yi jinjina da godiya ga mai girma gwamna dangane da gudunmawar shanu da kayan abinci da ya aike babban gidan Yari na Jiha domin jiyar da ɗaurarru daɗin Sallah!

Ya kuma ƙara da yabo kan wannan tsarin afuwa da mai girma gwamna ya ke da shi domin ba wa ɗaurarrun da aka yi wa afuwa ƴanci da walwalar komawa cikin iyalansu.

Ya yin da ya waiwaici wuraren jinyar matan da su ka gamu da lalura kuwa, (VVF Hostel, Kwalli), gwamna Ganduje ya yi alƙawarin samar da muhallin da za a riƙa ɓa su horo kan sana'o'in dogaro da kai a zamanance domin su samu damar tsayuwa da ƙafafunsu da zarar sun samu lafiya an sallame su.

Kamar yadda sakataren dindindin na ma'aikatar kula da harkokin mata da walwalar jama'a, Auwalu Umar Sanda ya bayyana, kimanin mata (825) ne su ka samu kulawa a wurin daga watan farko (Janairu) na wannan shekara zuwa yau.

Ya kuma ƙara da godewa gwamna Ganduje kan yadda ya ke ba su dukkan haɗin-kai da goyon baya kan wannan aiki.

Da ya ziyarci gidan Yara na Goron Dutse kuwa, gwamna Ganduje ya bayyana irin ƙoƙarin da ya ke na ganin kowane Yaro ya na zuwa makaranta tare da ba da Ilimi kyauta a Jihar Kano. Gami kuma da jan hankali ga yaran da ka da su fidda rai da saduwa da iyayensu, su zamto masu ɗa'a da halin ƙwarai yau da kuma nan gaba.

A ya yin ziyarorin, gwamna Ganduje ya samu rakiyar Sanata Barau I. Jibrin. Da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji. Da shugaban ma'aikata, Dakta Kabiru Shehu. Da Shugaban jam'iyyar APC na Jiha, Alhaji Abdullahi Abbas (Ɗan Sarki). Da Dattijon Jam'iyya, Alhaji Nasiru Ali Ƙoƙi. Da Ɗan Majalissar Wakilai na Gwale, Alhaji Lawan Kenƙen. Da kuma tsaffin kwamishinoni da matemaka na musamman.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment