Wednesday, 7 August 2019

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Na Cigiyar Yaron Da Ya Zana Hotonsa Domin Tallafa Masa

"Ina cigiyar wannan yaron da ya zana hoton mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, an ce dan jihar Gombe ne kamar yadda editan jaridar RARIYA Aliyu Ahmad ya ruwaito. Idan an samo yaron za mu tallafawa karatunsa na sakandire, idan ya kammala kuma za mu biya kudin karatunsa na jami’a a makarantar da ya samu gurbin karatu a kasar nan ko kuma mu ba shi Scholarship a Jami’armu ta Skyline Nijeriya. 

Burin mu wannan yaron ya samu ilmin da zai cimma burinsa na kwarewa a fagensa na zane-zane. Allah ya bar Sarki da masoyansa".

Daga Sa’adatu Baba Ahmad

...tuni dai RARIYA ta mika lambar yaron ga Hadimar Sarki Sanusi II, wato Sa'adatu Baba Ahmad domin tuntubarsa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment