Wednesday, 14 August 2019

Sarkin Kano ya sake samun Babban mukami daga kasar Canada


Wata kungiyar kasar Canada dake fafutukar samar da ingantaccen ilimi ga kasashen masu karamin karfi me suna, 1Million Teachers Inc ta nada me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II a matsayin shugaban kwamitin dake bata shawara na Najeriya.

Hakanan Sarki Sanusi zai kuma zama memba na kwamitin gudanarwar uwar kungiyar.

Shugaban kungiyar, Hakeem Subair ya bayyana farin cikinshi da nada Sarki Sanusi wannan mukami, a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar jiya, Talata ta bayyana cewa, Hakeem yace Shigar sarki Sanusi kungiyar tasu abune da zai kara musu kwarin gwiwa dan dama aninda suke nema shine mutane masu karfin fada aji da zasu taimaka wajan watsa manufofin kungiyar na ganin an samar da ilimi ga kowa musamman manya da yaran mata da kuma baiwa kungiyar shawara.

A karshe dai yace suna wa Satki Sanusi Maraba da shigowa kungiyar tasu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment