Monday, 12 August 2019

Shekara Shida yana zana jarabawar Shiga Jami'a ba ya ci amma daga karshe ya mutu bayan kammala Karatu

Ko wannan labari zai zama izna ga samarinmu 'yan mata masu ra'ayin sai sun kammala jami'a sannan su yi aure? Ko wannan labarin zai karfafa zuciyar matasanmu akan sa himma domin cimma burinsu?


Sunansa Godwin Idoko, wanda ake yi wa lakabi da Simon, ya fita da sakamako mai kyau da ake kira (fist class) a sashen binciken Sinadirai (wato Apply Chemistry) daga Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.

Ya rasu ne kwanaki kadan bayan kammala shirinsa na hidimar wasa (NYSC). 

Mamacin wanda ya rubuta jarabawar shiga Jami'a (Jamb) har kusan sau shida kafin ya samu damar shiga jami'a domin samun damar soma karatunsa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment