Saturday, 24 August 2019

Shekaru 22 bayan rasuwarshi: An hako gawar Nasir bata rubeba, likkafaninshi be yi datti ba

Allah sarki, wata alama dake nuna mutumin kirki da yayi rayuwa me kyau itace kaga gawarshi bata lalace ba tana nan yanda take shekaru aru-aru, akan samu haka wasu lokutan idan aka yi akasin tono kabari ba tare da shiri ba kamar yanda ya faru a kasar India.
An tono kabarin wani bawan Allah me suna Nasir Ahmad dake titin Attara, Beberu.

Wani abin karin mamaki shine shekarun Nasir 22 da rasuwa amma ko likkafanin marigayi Nasir be dauki dattiba ballantana jikinshi ya lalace.

Yanda aka hako gawar tashi kuma shine, ruwan sama aka yi kamar da bakin kwarya, sai ya bude wasu kaburbura shine aka je gyara. Ana gyara sai aka ga haske a kabarin Nasir shine daka tono aka ga babu abinda ya samu gawarshi bata rube ba.

Da dama mutanen yankin sun bayyana wannan abu da cewa mu'ujizace da Allah.

An kuma haka wani kabarin inda aka sake Binne Nasir, kamarbyanda NAN ta ruwaitoKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment