Tuesday, 6 August 2019

Shugaba Buhari Ya bayyana ranar da zai rantsar da sabbin ministoci

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fitar da jadawalin shirye-shiryen rantsar da sabbin ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada.


Babban Sakatare a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Babatunde Lawal, ya bayyana cewa za ayi ganawa ta musamman da sabbin ministocin domin tattaunawa na sanin makaman aiki a ranakun 19 da 20 na watan Agusta.

Ranar 21 kuma gaba daya za a hallara a fadar shugaban kasa inda za a rantasar sabbin ministocin sannan kowa ya san ma’aikatar da zai yi aiki.

Cikin wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sun hada da tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom Godswill Akpabio, Babban Lauya Festus Keyamo, tsohon gwamnan jihar Benuwai George Akume da wasu 40.
Premiumtimeshausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment