Saturday, 24 August 2019

Shugaba Buhari ya gana da Gwamna Zulum bisa Harin Boko Haram

A kokarin sa na inganta harkar tsaro a jihar Borno, Mai Girma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja dangane da harin Boko Haram a kananan hukumomin Gubio, Magumeri da Konduga wanda suka auku cikin makon nan.


Malam Isa Gusau shine mai magana da yawun Gwamnan, inda ya bayyana cewa  Zulum ya samu ganawa da Buhari a cikin Villa ne jim kadan bayan idar sallar Juma'a a jiya.

Gusau yace: "A ganawar, Zulum ya bayyanawa Buhari yanda harin Boko Haram din ya gudana inda ya daidaita garuruwa a daren laraba a Gubio da Magumeri, da kuma harin da aka kai a kauyukan Wanori, Kalari da Dalori dake Karamar Hukumar Konduga".

Ya kara da cewa: A tattaunawar, Zulum ya bayyana yanda Boko Haram suke sake zage damtse wurin ci gaba da kai hare-hare a yankin arewacin jihar, inda ya nemi daukin gaggawa daga Gwamnatin Tarayya don tabbatar da tsaro a jihar Borno dama sauran yankunan arewa maso gabashin Nigeria.

Da misalin karfe 4pm na yamma Zulum ya fito daga ganawar inda ya wuce ya kara ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo duk game tsaron, inda a gefe guda kuma ya halarci taron Majalisar tattalin arziki na Kasa.

Idan za'a iya tunawa dai, Gwamna Zulum ya kai ziyarar ran gadi a Gubio sau biyu a ranar 11 da 13 na watan ogustan wannan shekarar, inda ya tattauna da Kwamandan Rundunar Lafiya Dole dake yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nigeria Mejo Janar Benson Akinroloyo da Birget Kwamandan dake kula da shiyyar Gubio.

Muna addu'ar Allah ya bamu zaman lafiya mai daurewa. Amin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment