Saturday, 24 August 2019

Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Japan

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Japan Gobe, Lahadi idan Allah ya kaimu inda zai halarci taron kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da kasar ta Japan karo na na 7.Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a gurin taron sannan zai kuma halarci wasu taruka na shuwagabannin kasar ta Japan da wasu kamfanonin kasar dake da jari a Najeriya.

Gwamnonin jihohin Borno, Kwara da Legas da wasu ministoci da kuma wasu manyan jami'an gwamnatine zasu wa shugaba Buhari rakiya,kamar yanda sanarwar me magana da yawunshi, Femi Adesina ya bayyana.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment