Pages

Friday 23 August 2019

Shugaban kungiyar kare muradun Inyamurai ya sha da kyar bayan cewa duk Inyamurin da zai taba Bahaushe ya fara kasheshi tukuna

A wani bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo an ga shugaban kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo, Chief John Nnia Nwodo yana bayanin cewa duk wani Inyamurin dake son taba Bahaushe to ya fara kasheshi tukuna.



Nnia Nwodo ya kara da cewa, suna son kasa me hadain kai da zaman lafiya da 'ya'yansu nam gaba zasu taso su yi Alfahari da ita.

Kalli bidiyon anan:

Saidai bayan wancan bayaninashi, wasu matan inyamurai sun kunyatashi ta hanyar zagi da cin zarafi a wajan wani taro daya halarta kamar yanda za'a iya gani a wannan bidiyon na kasa:






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment