Wednesday, 21 August 2019

Sojan Da Ya Bada Umarni Aka Harbe 'Yan Sanda Uku Don Kubutar Da Mai Garkuwa Da Mutane

Hotunan gidan da aka kama 'dan ta'adda shugaban masu garkuwa da mutane na jihar Taraba Hamisu Bala Wadume a birnin Kano, da hoton abokinsa jami'in soja mai mukamin Kyaftin (Captain) Balarabe Tijjani wanda ya bada umarni aka hallaka kwararrun 'yan sanda guda uku na rundiar IGP-IRT karkashin jagorancin DCP Abba Kyari da farar hula guda daya tare da raunata sauran jami'an 'yan sanda.


Abinda wannan jami'in soja ya aikata na cin amanar tsaron Nijeriya bai shafi sauran sojojin kasarmu Nijeriya ba, don haka kuskure ne a kalli sauran sojoji da irin laifinsa, a kowace ma'aikata ko hukuma na tsaro ana samun gurbatattu maciya amana, sai dai bai kamata a dinga ba su mafaka ba, kamata ya yi maciya amana a dinga tsame su daga aiki.

Tabbas wannan abin da ya faru na kisan jami'an 'yan sanda ya taba zuciyar duk wani mai kaunar zaman lafiya a Nijeriya, duk da kasancewar sojan musulmi amma abinda ya aikata cin amanar kasa ne da zaman lafiya, kuma zalunci ne, ba ma goyon bayansa akan haka, muna fata bayan sakamakon bincike a zartar masa da hukuncin da ya dace bisa doka da duk wanda yake da hannu a cikin al'amarin

Yaa Allah Ka cigaba da tona asirin maciya amanar tsaron Nijeriya.

Allah Ka ba mu zaman lafiya a kasar mu Nijeriya. Amin.
DattiAssaalafyKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment