Thursday, 8 August 2019

Sojojin Najeriya sun kashe 'yansanda 3 tare da jikkata 1

Rahotanni dake fitowa daga jihar Taraba sun yi nuni da cewa, dakarun sojoji sun bude wuta wa tawagar yan sanda a karamar hukumar Ibbi inda suka kashe mutum uku.


Rahotannin sun yi nuni da cewa jami'an 'yan sandan suna dauke da kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda suka kamo da niyyar kai shi cibiyar yan sanda dake Jalingo.

Sojojin sun bude wuta kai tsaye akan tawagar yan sandan, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar yan sanda uku tare da wani farar hula da kuma jikkata wasu.

A cikin wani sanarwa da kakakin hukumar 'yan sanda Frank Mba ya fitar, ya bayyana cewa bude wuta da sojojin suka yi akan yan sanda yayi sanadiyyar tserewar kasurgumin mai laifin da suka kamo.

Tuni shugaban hukumar yan sanda yayi umurnin binciken gaggawa akan lamarin.

Abun tambaya a nan shine, menene zai kawo wannan ganganci da zai yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro da kuma tserewar kasurgumin mai laifi?

Shin Sojoji da 'yan sanda duka suna yiwa Nijeriya aiki ne ko kuma akwai wani manufa na daban?

Mafi girman abunda kuskuren nan ya haifar bayan asaran rayuka shine ' yaci ga dan ta'adda mai garkuwa da mutane. Yanzu haka yana cikin al'umma. Allah kadai yasan me yake kullawa.

Allah ya kyauta.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment