Wednesday, 28 August 2019

SOYAYYAR KARYA TA 'YAN ZAMANI

Yaran yanzu don ana soyayya ba abun kunya ba ne su rungumi juna a gaban kawaye da abokai wani lokacin har da iyaye ma,  haka nan gurin taron bukukuwa a gaban iyaye za su rungumi juna har da sumbata ana ihu da tafi. 


To ku sani wallahi wannan shine tushen rashin albarka a aure, an gama watsar da duk albarkar da mutumcin a titi, me ku ke tsammanin zai faru idan an yi auran? 

Irin wannan aurarraki su ne ake caka wuka, su ne ake dukan abokin aure, shine ake zagin juna har da iyaye, shine ba a ganin darajar juna,  shine ake zargin juna kullum cikin rigimar kar mace ta rike babbar waya shi kuma miji yana ta boyon waya da saka 'password' masu zafi,  shine bai cika shekara ko watanni ke fita daga ran maauratan har ya mutu cikin kankanin lokaci. 

To wallahi ku sani idan har ba mu gyara tarbiyyarmu da ta yayanmu ba Allah ba zai aiko mala'iku su gyara mana ba, za mu ci gaba da zama cikin rudu da rudani.
Daga Fauziya D. SuleimanKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment