Tuesday, 13 August 2019

TAFIYAR EL-ZAKZAKY: Yadda Buhari ya yi fatali da tsauraran ka’idojin El-Rufai

Kwararan alamomi sun nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya gwasale Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai, ya bada umarnin a bar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tafiya neman magani tare da matar sa Zeenat, ba tare da cika ka’idojin da gwamnatin Kaduna ta bijiro da su daga bayan bada belin su ba.


Da yammacin yau ne El-Zakzaky da matar sa tare da wasu tsirarun jami’an tsaro suka lula kasar Indiya a jirgin Emirate.

PRNigeria ta ji daga wata majiyar jami’an tsaro cewa ba mamaki Shugaba Buhari ya daga wa El-Zakzaky kafa tare da bada umarnin ya fita neman maganin tunda kotu ta rigaya ta bada belin sa, ba tare da cika tsatstsauran ka’idojin da gwamnatin Kaduna ta kakaba masa ba.

Zai iya kasancewa jami’an leken asirin gwamnati ne suka bada wannan shawara ta yin fatali da ka’idojin El-Rufai.

Hukumar Jami’an Leken Asiri (NIA) da kuma ta ‘Yan Sandan Ciki na DSS sun rika cuku-cukun ganin an warware wannan kwatagwangwamar tafiyar El-Zakzaky ta bayan fage, ganin cewa sun shawarci Fadar Shugaban Kasa dangane da muhimmancin cancantar amincewa da bin umarnin kotu.

Hakan ya kara biyo baya ne ganin kuma cewa an yi amfani da tattaunawar diflomasiyya da wasu kasashe, ciki har da gwamnatin Iran a kan lamarin.

GWAMNATI TARAYYA TA GWASALE SHARUDDAN ‘SHIRMEN’ GWAMNATIN EL-RUFAI –Femi Falana

Da ya ke zantawa da PRNigeria, lauyan El-Zakzaky, Femi Falana, ya shaida wa jaridar cewa gwamnatin tarayya ta yi wancakali da sharuddan ‘shirmen’ da Gwamnatin Jihar Kaduna ta nemi kakaba wa shugaban mabiya Shi’a din da kuma matar sa Zeenat kafin a bari su tafi Indiya a yau Litinin.

Falana ya ce sharuddan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kakaba wa El-Zakzaky kwata-kwata ba ‘ya’yan cikin dokar kasa ba ne, ‘ya’yan agola ne Kaduna ta nemi maidawa ‘ya’yan dokar kasa na halas.

Sanannen lauyan ya ce tunda kuwa sharuddan sun duk harankazama ce, ba su cikin ka’idojin bada beli da tafiya kotu wadanda kotun Kaduna ta gindaya, babu yadda za a yi kotu ta amsa bukatar gwamnatin Kaduna, har ta amince da tsauraran sharuddan.

Falana ya kara hasken cewa babu yadda za a yi ma gwamnati ta tsaya bin wasu sharudda da gwamnatin Kaduna ta kakaba, domin DSS sun rigaya sun fito sun bayyana wa duniya cewa za su bi umarnin kotu, su saki El-Zakzaky da matar sa su fita zuwa Indiya neman magani.

Gwmnatin Kaduna dai ta bada sanarwar amincewa da belin El-Zakzaky da kotu ta yi, amma kuma ai ta bijiro da wasu tsauraran ka’idoji, wadanda masana shari’a ke ganin shiga hurumin kotu ne, kuma ba su cikin ka’idoji.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment