Thursday, 8 August 2019

Tsohon ma'aikacin gwamnati ya dawo da karin miliyan 1 da akamai kan kudin sallamarshi bisa kuskure


Allah sarki, na gari basa taba karewa, Wani tsohon ma'aikacin gwamnati a jihar Bauchi da aka biyashi kudin sallama da doriyar miliyan daya akan ainahin kudin da ya kamata a biyashi, ya mayar da karin miliyan dayar da aka mai ga gwamnati.Da yake bayyana yanda lamarin ya faru, Shugaban kungiyar tsaffin ma'aikatan gwamnati reshen jihar Bauchi, Habu Gar yace, yana jawo hankalin gwamnatin jihar Bauchi da ta mayar da hankali kan yanda ake biyan tsaffin ma'aikata hakkokinsu ta yanda baza a samu matsalaba, yace an biya wani karin kashi 500 akan kudin da ya kama a bashi, kuma in banda gaskiyar daya nuna wajan dawo da kudin da ba za'a san inda miliyan dayar da aka bashi ta tafi ba.

Da yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya, Gar ya bayyana cewa tsohon ma'aikacin da ainahin kudin da za'a bashi dubu 200 ne, an bashi cek din miliyan 1 da dubu 200.

Bayan da ya kai Cek din banki aka biyashi kudin sai yayi gaggawar dawowa da gwamnati da karin miliyan 1 da aka mai.

 
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment