Wednesday, 7 August 2019

Tunda an hanani mukami a majalisa, na koma raino>>Abdulmumin Jibrin

Dan majalisar wakilai me wakiltar mazabun Kiru da Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin kenan a wadannan hotunan nashi yayin da yake rike da diyarshi, yayi barkwanci inda ya bayyana cewa ya zama shugaban masu raino na kasa.Jibrin ya kara da cewa tunda be samu mukamin kowane kwamiti ba sannan kuma wasu sunce shi ba dan jam'iyya bane shi yasa ya koma aikin reno.

Ya karkare da cewa diyarshi, Farha ta fara girma.

Muna fatan Allah ya rayata rayuwa me Albarka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment