Sunday, 25 August 2019

Turmutsutsu a wajen chasu ya kashe mutane 5 a Aljeriya

Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon turmutsutsun da ya afku a wajen chasun da shahararren mawaki Abdurrauf Derradji da aka fi sani da "Soolking" a Aljeriya.


A daren Juma'ar nan mawakin Rap Derradji ya chashe Algiers Babban Birnin Aljeriya inda dubunnan mutane suka taru a filin wasanni na 20 August 1955.

Sakamakon yadda a lokaci guda mutane suka kwarara zuwa kofar shiga filin wasan ya janyo turmutsutsun da ya yi ajalin mutane 5.

Duk da wannan abu da ya afku ba a soke chasun ba kuma an yada shi kai tsaye a gidan talabijin din Aljeriya.

Sollking Bafaranshe dan asalin Aljeriya na da masoya da dama a tsakanin matasan Aljeriya da na arewacin Afirka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment