Sunday, 25 August 2019

Yadda Jihar Sokoto Ta Tara Manyan Nijeriya Wuri Guda A Yayin Bikin 'Yar Sarkin Musulmi

A yau garin Sakkwato ya dauki manyan baki daga ciki da wajen kasar nan domin halartar shaidar auren diyar Mai Alfarma Sarkin musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III da Alh. Mahmud Isa Yuguda dan tsohon Gwamnan Bauchi.  Kafin shaidar auren garin Sakkwato ya sha kawa da tsaftace ta kulawar ma'aikatar muhalli ta jihar, karkashin kulawar matashin kwamishina Sagir Bafarawa. 

Shaidar auren ya samu halartar manyan Sarakuna, malammai, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, ma'aikatan Gwamnati da sauran mutanen gari.

 "Mun jima ba mu ga baki irin na yau ba" cewar wani mazaunin garin Sakkwato.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment