Wednesday, 7 August 2019

'Yan majalisa sun kori abokiyar aiki kan shayar jaririyarta


Kenya
A ranar Larabar nan ne a zaman Majalisar Dokokin kasar Kenya aka fitar da wata 'yar majalisa bayan da ta halarci zaman tare da jaririyarta 'yar wata biyar.


Dan majalisa dan'uwanta ne ya yi kira ga saje na majalisar da ya fitar da Zuleika Hassan daga zauren.
Bayan da aka kore 'yar majalisar daga zauren, ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta je da jaririiar tata zauren shi ne wata matsalar gaggawa da ta same ta.
A ganin wasu mutane dai abin mamaki ne cewa an kore ta daga majalisar domin ta je da jaririyarta a yayin da ranar shayar da nonon uwa ta duniya ke kara karatowa.

Wasu daga cikin 'yan majalisar maza sun soki hukuncin da Zuleika Hassan ta dauka na zuwa da jaririyar tata, a yayin da shi kuma shugaban masu rinjaye, ya bayyana abin da ta yi a matsayin abin kunya.
'Yan majalisar sun ta yin hayaniya da tsawa kan cewa lalai sai takawarar ta su ta fice, yayin da shugaban majalisar yake cewa su saurara, tare da kuma bata umarnin fita ba tare da bata lokaci ba.
A shekara ta 2017, 'yan majalisu a Kenya sun amince da wani kudurin doka wanda zai tilasta wa duk wanda zai dauki ma'aikata, samar da daki na daban, inda iyaye mata za su iya shayar da jariransu.
To sai dai har yanzu majalisar ba ta yi wannan tanadin ba har yanzu.
BBCHausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment