Wednesday, 14 August 2019

Yanayin da muke ciki a India ya fi na Najeriya muni>>Zakzaky

Jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi ta IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya koka akan yanda kasar Indiya ke kula dashi da matarshi inda yace yanayin da suke ciki a kasar India yafi muni fiye da yanda aka tsaresu a Najeriya.A wata sakon murya da Zakzaky ya saka da taita yawo a shafukan sada zumunta anji yanda yace kasar India ta kauce kan alkawarin da akayi za'a dubashi bayan da suka sauka a kasar.

Yace bayan saukarsu an saka jami'an tsaro sosai rike da muggan makamai da kuma wakilan ofishin jakadancin najeriya suma duk suna asibitin, yace yanayin kamar suna gidan yari.

Ya kara da cewa kuma an canja likitocin da suka amince su dubasu inda aka kawo wasu sabbi da basu san dasu ba, dan haka yake neman Dawowa Najeriya.

Wata kungiya dake rajin kare hakkin musulmi, IHRC ta bayyana cewa kasar India na rike da Zakzaky a matsayin me laifine wanda kuma zahiri a kasarshi babu wata kotu da ta tabbatar da cewa shi me laifine.

Lamarin yayi kamari ta yanda har kasar India ta bukaci Zakzaky kodai ya amince a dubashi ko kuma ya bar mata kasarta.

Saidai rahotannin dake fitowa da yammacinnan na cewa Kasar ta India ta amince da bukatar Zakzaky na likitocin da ya sani su duba lafiyarshi data matarshi Zeenat.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment