Tuesday, 20 August 2019

Yanda ake ciki kan dambarwar Tafiyar Neymar daga PSG

Jaridar Le Parisien dake Faransa ta zargi kungiyar Barcelona da yin karya gami da yaudara, bisa nuna muradin sake kulla yarjejeniyar da tsohon dan wasanta Neymar, wanda PSG ta saya daga Barcelonan a shekarar 2017, kan euro miliyan 222.
Rahoton da jaridar ta Le Parisien ta wallafa, yace Barcelona ta bayyana aniyar bogi ta maido da tsohon dan wasan nata ne kawai domin dada-dawa kaftin dinta Lionel Messi kafin soma kakar wasa ta bana.

Barcelona ta soma tuntubar PSG kan Neymar ne, bayan da Messi ya bukaci hakan, inda kungiyar ta Barcelona ta yiwa PSG mika mata euro miliyan 100 da kuma dan wasanta Philippe Coutinho, a matsayin musayar Neymar, tayin da bai samu amincewa ba, inda PSG tace tana bukatar akalla tsabar kudi euro miliyan 200 kafin sakin dan wasan mafi tsada a duniyar tamaula.

A gefe guda kuma tuni abokiyar hamayyar Barcelona, Real Madrid ta yiwa PSG tayin biyanta euro miliyan 100 da mika mata ‘yan wasa uku, Varane, Isco, da kuma Marcelo.

A makon gobe ake sa ran Barcelona ta gabatarwa da PSG sabon tayi kan sake sayen Neymar.

Itama dai Juventus ta shiga sahun zawarcin Neymar kamar yanda Rahotanni suka bayyana daga AS, inda take shirin bayar da tauraron dan wasanta, Dybala wanda yake akan Yuro miliyan 80 da kuma kudi Yuro miliyan 100 dan PSG ta bata Neymar. Watau dai PSG ta samu Yuro miliyan 180 kenan da take nema akan Neymar idan wannan magana ta tabbata.

Saida a wasan da PSG ta buga da Rennes wanda Rennes din ta lallasata da ci 2-1, Neymar din be buga wasa ba saboda raunin da yake dashi a gwiwa.

Bayan kammala wasan, Kocin PSG Tuchel ya bayyana cewa ba zasu saki Neymar ba sai sun samu madadinshi.

Koma dai ya zata kasance akan dambarwar Neymar dake da mafarkin barin PSG kamar yanda rahotanni suka nuna zamu gani idan lokaci yazo.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment