Tuesday, 6 August 2019

Yanda salon murnar cin kwallona ya samo asali>>Ronaldo


Cristiano Ronaldo yayi bayanin asalin murnar cin kwallonshi
Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo yayi bayanin yanda murnarnan da yake yi idan yaci kwallo ta tashi sama yayi juyi ya watsa hannuwa ta samo asali.Ronaldo yace salon murnar cin kwallon nashi ta samo asaline daga wasan sada zumunta da suka taba bugawa da kungiyar Chelsea a kasar Amurka a shekarar 2013 lokacin Jose Mourinho na horar da kungiyar kuma suka cisu 3-0, Ban ma san yanda aka yi na yi hakan ba, Ronaldo ya gayawa shafin Youtube na Soccer.com a hirar da suka yi dashi.

Na ci kwallo ne kuma kawai sai naga na yi hakan, a gaskiya kawai inaga abin daga Allahne, injishi.

Daga nan kuma sai abin ya birgeni shine a duk sanda na ci kwallo sai in rika yin hakan, na ga cewa masoyana suna son abin kuma sukan tunani dashi shiyasa na ci gaba da yinshi, inji Ronaldo.

Da aka tambayeshi dan wasan da zai so buga kwallo dashi, sai yace marigayi Eusebio, watau tsohon dan kwallo Portugal da ya bugawa Benfica wasa. Yaci kwallaye 733 a wasanni 743 daya buga kuma na hannun damar Ronaldonne, ya mutu a shekarar 2014.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment