Monday, 12 August 2019

Yau za a fitar da Zakzaky daga Najeriya>> IMN

Kungiyar IMN mai bin mazhabat Shi'a a Najeriya ta ce a yau Litinin ne za a fita da shugabanta Sheikh Ibrahim Zakzaky daga kasar zuwa Indiya don neman magani.


Mai Magana da yawun Kungiyar Ibrahim Musa ne ya tabbatar wa da BBC cewa "shirye-shirye sun kammala kuma zuwa an jima zai tashi tare da mai dakinsa da wasu jami'an gwamnati ta filin jirgin saman Abuja."

Ya ce sun "samu biza da dukkannin takardun da ake bukata kafin tafiyar."

Sai dai bai yi karin haske ba game da lokacin da jirgin zai tashi.

Babu wani bayani a kan ko an cika sharuddan da gwamnatin jihar Kaduna ta gindaya kafin ta amince da tafiyar jagoran na IMN.

Mun yi kokarin jin ta-bakin gwamnatin, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba; har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan bai amsa kiran da muka yi ta yi masa a waya ba.

Akwai rahotannin da cewa a jiya Lahadi ne aka dawo da shi Abuja daga jihar Kaduna, inda yake tsare.
Wannan yana zuwa ne mako guda bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta ba malamin addinin damar zuwa kasar Indiya neman magani bayan gindaya masa wasu sharudda.

Bayan hakan ne kuma gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da bukata gaban babbar kotun jihar ta neman a sanya "wasu sharudda game da damar tafiya neman maganin" da kotun ta ba Zakzaky da mai dakinsa Zeenat.

Gwamnatin ta zayyano wasu sharudda bakwai ne da take so a cika gabanin tafiyar malamin addinin kasar waje.

Sai dai lauyan mutanen biyu Barrister Haruna Garba Magashi ya shaida wa BBC cewa za su kalubalanci matakin gwamnatin, yana mai cewa "ta yi ne domin kawo tsaiko kan tafiyar malamin neman magani".
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment