Saturday, 17 August 2019

ZA A KAMA FITATTUN MAWAKAN KANNYWOOD - Freedom Radio

Bayan kama shahararren Daraktan Fin-finan Hausa Sunusi Oscar 442, da Hukumar Tace Finafinan jihar Kano ta yi. Gidan rediyon Freedom mai zaman kansa a jihar ya kawo rahoton kama wasu fitattun mawakan Kannywood da ake zaton Hukumar zata kara kamawa. Mawakan wadanda suke nuna goyon bayansu ga siyasar tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso sun hada da:


1. Aminuddeen Ladan Abubakar da aka fi sani da ALAN WAKA.

2. Naziru Ahmad da aka fi sani da SARKIN WAKA mai kuma rike da sarautar 'Sarkin Wakar Sarkin Kano.

3. Misbahu Ahmad

4. Ali Artwork 

5. Mustapha Badamasi Naburuska 

A yayin da SARAUNIYA ta tunrubi Freedom sun tabbatar da cewa sun ji ta bakin Mawakan kuma sun tabbatar da wannan batu, sai ALA da wayarsa take a rufe. 

SARAUNIYA ta tuntubi Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano Isma'il Afakallahu domin jin gaskiyar lamari.

"Wannan labari ba gaskiya ba ne,  sai dai idan dama laifin suke aikatawa shine suke neman mafaka ko da za a kama su. Kuma hakan ba zai hana mu kama duk wanda ya aikata laifi ba".
Maje El-Hajeej Hotoro.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment