Thursday, 15 August 2019

Zakzaky ya sallami kanshi daga Asibitin India ya kamo hanyar dawowa Gida Najeriya

Rahotanni dake fitowa daga kungiyar Shi'a ta IMN sun bayyana cewa jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarshi Zeenat sun bar kasar India dan dawowa Najeriya saboda rashin adalcin da aka musu.Me magana sa yawun kungiyar, Ibrahim Musa ne ya bayyanawa Punch cewa katsalandan din da gwamnatin Najeriya ta rika yi a harkar duba lafiyar Zakzaky a kasar India ne ya jawo hakan sannan kuma dama can gwamnatin Najeriyar bata so zuwan zakzaky neman magani ba.

Ya kara da cewq Zakzaky da matarshi sun baro India suna kan hanyarsu zuwa Najeriya
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment