Tuesday, 6 August 2019

Zamu gaggauta kammala tashar jiragen ruwa ta tudu dake Kano>>Gwamnatin tarayya


Gwamnatin tarayya ta tabbatar da aniyarta na ganin ta kammala tare da fara aikin tashar jirgin ruwa ta kan tudu ta dake Kano. Wadda ake kira da Dala Inland Dry Port.Shugaban hukumar ayyukan raya kasa(ICRC), Chidi Izuwah Snr Ne ya tabbatar da hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido gurin aikin ginin tashar dake Zawaciki a karamar hukumar Kumbotso dake Kano.

Da yake jawabi a wajan ziyarar da ya kai, Chidi yace gwamnatin tarayya zata yi kokarin ganin ta kawar da duk wata matsala da ka iya kawo tsaiko wajan kammaluwar aikin tashar cikin gaggawa, yace tashar zata taimaka wajan saukaka harkar kasuwanci da kuma kawo ci gaban tattalin arziki.

Ya kara da cewa, tashohin jiragen ruwa dake gabar teku sun yi kadan dan haka gwamnati ke kokarin ganin ta samar da na kan tudu dan samar da ci gaba a kasarnan, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment