Wednesday, 7 August 2019

Zan kare muradun APC a zangon mulkina na biyu>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da 'yan majalisar jihar Bauchi na APC a fadarshi dake Villa babban birnin tarayya, Abuja.Hakanan shugaban ya kuma gana da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC a fadar tashi duk dai a yau, inda ya tabbatarwa da membobin jam'iyyar cewa zai saka muradun jam'iyyar APC a zuci wajan yanke shawarwari a zangon mulkinshi na biyu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa yana yabawa shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole bisa kokarin da yayi na bautawa jam'iyyar sannan kuma ya jawo hankalin 'yan jam'iyyar da su rika girmama kundin tsarin mulkin kasa.

Da yake nashi jawabin, shugaban APC, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ya jinhinawa shugaba Buhari sannan kuma babbar nasarar APC a babban zaben daya gabata shine a jihohin Kwara da Gombe duk da dai sun yi rashin nasara a wasu jihohin.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment