Thursday, 12 September 2019

Abinda Zlatan Ibrahimovic yawa wani da yayi kutse a filin wasa da wani dan wasa ya dauki hankula

A wasan da kumgiyar LAGalaxy ta Buga da kungiyar Colorado da aka tashi wasan Ana cin LAGalaxy 2-1, Zlatan Ibrahimovic ya dauki hankulan mutane saboda abinda yawa wasu 'yan kallo da suka yi kutse a filin da kuma wani dan wasan Colorado daya tambayeshi su yi canjin riga.
Daya daga cikin wanda suka yi kutse a filin yana zuwa daidai Movic sai ya fadi kasa, ko kallonshi Movic din bai yi ba, hakanan shima na biyun yayi kokarin kama Movic amma kamin ya kai gareshi sai jami'in tsaro yayi ram dashi.

Daya daga cikin 'yan wasan Colorado ya biyo Movic yana son su yi canjen riga amma shima yana ta mai magana ya shareshi.

Abin ya dauki hankula.

Kalli yanda lamarin ya faru a cikin bidiyon da shafin kumgiyar ta LAGalaxy ta wallafa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment