Tuesday, 17 September 2019

Afirka ta Kudu ta nemi gafarar Najeriya

Afirka ta Kudu ta nemi gafarar Najeirya a kan hare-haren kin jinin bakin da aka kai wa 'yan Najeriyar da ke kasar.


Jakada na musamman na gwamnatin Afirka ta Kudu, Jeff Radebe, ya gabatar da takardar neman afuwar a madadin Shugaba Cyril Ramaphosa, a wata ganawa da yi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Da alamu gwamnatin Afirka ta Kudu na kokarin kyautata alakarta da sauran kasashen Afirkan wadanda hare-haren kin jinin baki a Afrika ta Kudun ya shafa.Jami'in na Afirka ta Kudu, ya shaida wa Shugaba Buhari a Abuja cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu, kuma ya ce tana daukar kwararan matakai.

A yayin da Afirka ta Kudu ta dauki wannan mataki, Najeriya na ci gaba da kwashe 'yan kasarta daga Afirka ta Kudu.

Ana sa ran isowar wani rukuni na 'yan Najeriya 319 daga Afirka ta Kudu a filin jirgin sama da ke Legas a ranar Talata.

Sai dai Shugaba Buhari ya tabbatar wa jami'in cewa za a kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A makon da ya gabata ne ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Laraba cewa bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a kashe dan Najeriya ko daya ba a rikicin.

Sai dai ya ce gwamnatin na duba yiwuwar yi wa jakadan kasar a Afirka ta Kudu kiranye tare da neman diyya ga sana'o'in Najeriya da aka lalata.

Najeriya dai ta janye daga Taron Tattalin Arziki na duniya da ya gudana a Afirka ta Kudu a makon da ya gabata bisa hare-haren.

Ta gargadi 'yan kasarta daga "ziyartar wuraren da rikici ka iya barkewa" a Afirka ta Kudu har sai an samu zaman lafiya.

Ita kuma Afirka ta Kudu ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya na wucin gadi bisa harin ramuwar gayya da aka kai a Najeriyar.

Tun ranar Lahadi 8 ga watan Satumba wasu gungun mutane suka fasa shagunan baki a Afirka ta Kudu tare da sace kayan da ke cikinsu a birnin Johannesburg.

Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce abin kunya ne ga kasarta.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment