Friday, 13 September 2019

A'isha Buhari ta bukaci a rika saka mata sojoji cikin masu yakar matsalar tsaro

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta bukaci da a rika saka sojoji mata cikin aikin samar da zaman lafiya na zahiri ba a barsu da aikin ofis ba kawai.A'isha ta bayyana cewa daya daga cikin dalilan matslar matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya ta ki ci ta ki cinyewa shine rashin saka mata sojoji a yi aiki tare dasu wajan wanzar da zaman lafiya.

A'isha ta yiwannan jawabine a wajan taron mata sojoji da aka yi a kwalejin tsaro ta kasa dake Abuja.

A'isha Buhari ta bukaci a canja tsarin dokar data iyakance matan sojoji da aikin Ofis kawai.

Saidai a nashi martanin, shugaban ma'aikatar tsaro ta kasa, Gabriel Olanisakin ya bayyana cewa rundunar tsaron Najeriya ta cimma samun saka mata a ayyukan tsaro da kashi 27.7 cikin dari fiye da kashi 17 cikin dari da majalisar dinkin Duniya ta bukata.

Ya kara da cewa ana baiwa mata sojoji dama iri daya data maza.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment