Wednesday, 11 September 2019

Akwai Alamu Kotu Ba Za Ta Yi Mana Adalci Ba>>Buba Galadima

SHARI'AR ZABEN 2019

Injiniya Buba Galadima ya ce ba ya tunanin za a samu hukuncin adalci a kotun karar zabe a yau Larabar.


Galadima wanda ya ke magana a madadin kan sa ba jam’iyyar PDP ba, ya ce a yadda tarihin lamarin shari’ar zabe yake a Nijeriya, ya ga take-taken jami’an tsaro da sauran lamura sun nuna ba wani adalcin da za a samu.

Buba Galadima ya ce sai wanda bai fahimci take-taken lamuran ba ne zai yi irin wannan tunanin na jiran sai an yanke hukunci kafin ya gane inda a ka dosa. Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment