Monday, 9 September 2019

Almajiran Sheik Dahiru Bauchi Sun Shiryawa Gwamna Bala Mohammaed Addu'ar Cika Kwanaki Dari A Ofis

Almajiran Shekh Dahiru Usman Bauchi sun shirya gagarimin taron addu'a ga Gwamnan jihar Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi) kan cika kwanaki 100 a ofis.Shekh Dahiru Usman Bauchi ne ya jagoranci yin addu'o'in yadda mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya kasance Babban bako na musamman a wajen taron.

Shekh Dahiru Usman Bauchi ya roki Allah ya kare Gwamnan jihar Bauchi sannan ya bashi Dubbannin nasarori Domin kawo ma jihar Bauchi da al'umman ta cigaba mai ma'ana*

Daga ofishin babban mai tallafawa Gwamnan jihar kan kafafen yada labarai Mukthar Mukhtar Gidado

Hotuna
Shaharuddin Muazu GalajeKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment