Monday, 16 September 2019

Amurka Na Iya Mayar Da Martanin Harin Da Aka Kai Wa Saudiyya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce sojojin Amurka sun “kintsa da cikakkun makamai” don mayar da martani akan hare haren da aka kai a daya daga cikin matatun man Saudiyya mafiya girma, da kuma wurin da ya fi samar wa duniya danyan mai.


“Mu na da hujjar yin imanin cewa mun san wanda ya aikata," abin da Trump ya rubuta kenan ta kafar Twitter jiya Lahadi da yamma. Shugaban kasar ya kuma kara da cewa yana jira ya ji daga Saudiyya game da wadanda su ka yi imanin su suka shirya harin kuma “a bisa wane sharadi zamu dauki mataki.”

Tun da farko, Sakataran Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya wallafa wani sakon Twitter mai cewa “Yanzu Iran ta kaddamar da wani mummunan hari akan wurin da ake samar da makamashi a duniya," wanda bai yi la'akari da ikirarin 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran cewa su su ka kai harin da jirage marasa matuka ba.

Sai dai Iran ta kira zargin cewa ta na da hannu a harin da cewa "gagarumar karya ce."Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment