Friday, 13 September 2019

An Harbe Wata Matashiya Data Ziyarci Ma’aikatar Ministan Kudi A Nijar

Wannan al’amarin ya sa masu kare hakkin dan adam kiran hukumomi da su gaggauta gudanar da bincike don tantance ainahin mafarin wannan harbi.


Cikin yanayin kaduwa, a kullumin faruwar wannan al’amarine masu amfani da shafikan sada zumunta ke tafka mahawara daga yammacin jiya laraba zuwa yau, ganin yadda ba zato ba tsamani harsashi ya afkawa wannan matashiya mai suna Jamilatou, a yayinda ta ke kokarin gabatar da takardunta a ofishin ministan kudin kasa, da nufin a bata damar goge waraiki a fannin da ta karanta.

Faruwar wannan al’amari a dai dai lokacin da motocin shugaban kasa ke shirin wucewa, ya sa jama’a nuna dogarawan fadar ta shugaba Issouhou da dan yatsa.

Gudanar da bincike don tantance ainahin tushen wannan harsashi a shirin gano jami’in da ke da alhakin wannan harbi, wata hanya ce da za ta tilastawa dogarawan fadar shugaban kasa su shiga taytayinsu inji Abdou Elhadji wani dan rajin kare demokradiyya na kungiyar FSCN.

Hotunan da aka yada a shafikan sada zumunta na gwada wannan matashiya zaune hannunta 1 nade da bandeji, alamar dake nunin ta ji mummunan rauni.
VOAhausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment