Tuesday, 10 September 2019

An kai wa wani Masallacin Juma'a hari a Afirka ta Kudu

An kai wa Masallacin Juma'a na biyu hari a cikin mako guda a Afirka ta Kudu.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari da harasan wuta kan Masallacin Juma'a na Himayatul Islam dake yankin Hillbrow na garin Johannesburg.


Wani bangare na Masallacin Juma'ar ya kone.

Masallacin Juma'ar na Himayatul Islam na a yankin da a 'yan kwanakin nan ake kai wa 'yan kasashen waje hare-hare a cikinsu.

'yan sanda da suka fara gudanar da bincike sun kama mutane 2.

A ranar Larabar da ta gabata an kai hari kan Masallacin Juma'a na Katlehong dake Johannesburg.
TRThausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment