Saturday, 7 September 2019

An kama ma'aurata da laifin sayar da diyarsu a kasar China

A kasar China an kama wasu ma'aurata da suka sayar da diyarsu 'yar kwana 3 kaca da haihuws, wannan hoton na sama irin kyamarar nance ta CCTV ta dauki hoton mahaifin yayin da yake fita da diyar tashi dan ya kaiwa wanda suka siya.
Hukumomi sun samu rahoon cewa, Mr. Zhao y sayar da diyar tashine daga masu amfani da shafin yanar gizo bayan da wani abokin shi ya tallata a kafar sadarwar Wechat cewa idan da me son sayen jaririya yazo.

Mr. Zhao da matarshi sun bayyana wa 'yansanda cewa sun sayar da diyar tasu akan fan 5,700 ne saboda ba zasu iya kula da ita ba.

Suma ma'auratan da suka ayi diyar sun bayyana cewa sun yi aure tsawon lokaci basu samu haihuwa ba saboda rashin lafiya shiyasa suka yi hakan.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment