Tuesday, 10 September 2019

An kama uban daya jefa dan shi me wata 4 a Duniya cikin rafi

Jami'an tsaron Civil Defence a jihar Naija sun kama wani mutum me suna Mustafa Aliyu daya jefa danshi dan wata 4 a Duniya cikin wani rafi.Da aka tambayeshi dalilin wannan aiki nashi, Mustafa me shekaru 20 a Duniya ya bayyana cewa matarshi ta tafi ta barshi da yaron shi kuma bai san yadda zai kula dashi ba, ranshi ya baci amma a karshe yace be san abinda ya sameshi ba sharrin shedanne.

Lamarin ya farune a rafin Uti na karamar hukumar Borgu.

Kwamandan Civil Defence na jihar, George Edem ya bayyana cewa har yanzu ba'a gane jaririn ba


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment