Friday, 13 September 2019

An kama wadanda ake zargi da satar shanu 1000 a Kano

'Yan sanda a jihar Kano sun tasa keyar mutum uku da ake zargi da satar shanu 1000 inda suka kashe daya daga cikin mai shanun a wani daji da ke arewa maso yammacin Najeriya.


'Yan sandan sun kama Saidu Abdullahi mai shekaru 23 da Lawal Mohammed mai shekaru 25 da kuma Suleiman Abdullahi mai shekaru 30 inda suka tasa keyarsu a matsayin wadanda ake zargi.

Runduna ta musamman ta "operation Puff Adder" da ke karkashin hukumar 'yan sandan jihar sun hada kai ne da kungiyar Miyetti Allah domin kama wadanda ake zargi a babban dajin Falgore da ke Kano bayan sun shafe kwanaki bakwai suna nemansu a cikin dajin.Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmed Iliyasu ya shaida wa manema labarai a Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru cewa, an gano shanu da kuma makamai a hannun wadanda ake zargin.


Makaman da aka kwato a hannunsu sun hada da:

1. Bindigogi biyu kirar AK47 tare da harsasai 110.

2. Bindigogi uku kirar pump action da harsasai 22

3. Kayan sojoji kala biyu.

4. Wayoyin salula guda hudu.

Hukumar 'yan sandan sun kuma ce, za su bi sawun sauran barayin da suka tsere domin kama su, da gano sauran shanun da suka sace da makaman da ke hannunsu.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment