Saturday, 7 September 2019

An kama 'yar jarida da saurayinta saboda 'ta yi zina'

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da 'yan jarida a Morocco sun bukaci a sako wata 'yar jarida da aka kama bisa zargin ta zubar da ciki da tarayya da namiji alhalin ba ta da aure.


Dukkan laufukan biyu da ake zargin Hajar Raissouni da aikatawa manyan laifuka ne a dokokin Maroco .Lauyan da ke kare Hajar ya musanta dukkan zargin, inda ya ce ta je asibiti ne dan ganin likitan mata sakamon zubda jini da ta ke fama da shi.

A makon jiya ne aka kama 'yar jaridar bisa zargin yin ciki ba tare da aure ba, da kuma zubar da cikin. Ana kuma tsare da saurayin da Hajar za ta aura da wasu abokan aikinta uku, inda ake gudanar da bincike a kansu ko za a gano wanda ya yi mata ciki. 

Ana sa ran gurfanar da su a kotu ranar Litinin.Hajar 'yar jarida ce da take aiki da gidan jaridar Akhbar Al-Yaoum, kuma ta sha yin rubuce-rubuce kan batutuwan 'yan adawa.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce kamen yana da nasaba da aikin jaridar da take yi, amma masu shigar da kara sun musanta hakan.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment