Friday, 13 September 2019

An kusa fara jin dadin wannan gwamnati>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya shafe shekarun baya na mulkonshi waja ganin ya fitar da Najeriya daga matsin tattalin Arziki kuma ya samu nasarar yin hakan, saidai har yanzu ba'a gani a kasa ba.Shugaban ya sha alwashin ci gaba da tsare-tasaren shi dan intanta Rayuwar 'yan Najeriya.

Yayi wannan jawabine yayin ganawa da shuwagabannin kungiyar kwadago da suka kai mai ziyara a fadarshi.

“Duk da cewa ayyukan da muka gudanar sun fitar da Najeriya daga cikin halin matsin tattalin arziki, har yanzu ba a kai ga ji ko ganin alfanun su ko cin moriyar su ba tukunna.

“Amma dai nan da shekaru hudu masu zuwa dai kam za mu ci gaba da irin wannan kokari. Kuma da yardar Allah za mu fitar da milyoyin ‘yan Najeriya daga cikin kunci, fatara da talauci.”

Sannan kuma ya ce wadansu kalubale da gwamnatin sa ta gada, sun kasance ne matsala a yanzu, saboda gwamnatocin baya ba su maida hankali wajen gina rayuwar al’umma ba.

Ya yi korafin yadda masu masana’antun kan su da manyan kamfanoni masu zaman kan su suka kasa samar wa dimbin jama’a ayyukan yi, ta yadda za su taimaka wajen rage yawaitar marasa aikin da ake kara samu ta dalilin yadda al’umma ke kara yawa bakatatan.

Shi kuwa shugaban gamayyar kungiyoyin, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara maida maida hankali wajen kara samar wa ‘yan Najeriya hanyoyin samun walwalar rayuwa, ta yadda gwamnati kuma za ta guri kara wa fetur farashi.

Sannan kuma ya yi kira da a kai karshen batun fara aiki da karin albashi da hanzari.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment